Skip to content

Latest commit

 

History

History
306 lines (153 loc) · 18.4 KB

hausa.md

File metadata and controls

306 lines (153 loc) · 18.4 KB

BBC News Hausa

Yadda za ku gane jabun magani a kasuwa

Laraba 26 Faburairu, 2025 da 4:10:25 Safiya

NAFDAC ta ce tun bayan fara wani samame, a cikin mako biyu ta gano jabun magani da ya zarce tirela 10 a kasuwar Idumota da ke Legas, kudu maso yammacin ƙasar.

Mun ninka kason kuɗaɗen jihohi sau uku bayan cire tallafin mai - Tinubu

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai-tsaye.

Real Madrid na farautar Branthwaite, Neymar na son komawa Barcelona

Laraba 26 Faburairu, 2025 da 4:06:55 Safiya

Real Madrid ta matsa ƙaimi kan ɗan wasan tsakiya a Everton da Ingila, Jarrad Branthwaite. Manchester City na son saye ɗan wasan Newcastle da Ingila, Tino Livramento.

Yadda matsalar ƙwaya ke tilasta wa Ghana tsaurara matakan tsaron iyakokinta

Laraba 26 Faburairu, 2025 da 4:12:05 Safiya

Hakan dai ya biyo bayan wani rahoto na musamman na binciken kwakwaf da BBC ta yi ne mai suna BBC Africa Eye, wanda ya bankaɗo yadda ake safarar kwayar ta tramol daga kasar Indiya zuwa kasashen Afirka ta yamma

Matashin da mata ke son ya yi musu kitso

Laraba 26 Faburairu, 2025 da 4:13:59 Safiya

Gilbert Ogoniwari matashi ne wanda ya yi fice kan yadda yake rangaɗa wa mata kitso.

Ɓoyayyar taswirar da ka iya samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Laraba 26 Faburairu, 2025 da 4:13:13 Safiya

A shekarar 2008, Firaiministan Isra'ila na wancan lokacin Ehud Olmert ya buƙaci shugaban Falasɗinawa ya amince da maslahar samar da ƙasa biyu. Bai taɓa nuna wa wata kafar yaɗa labarai taswirar da ya zana ba - sai yanzu.

Tattalin arziƙin Najeriya ya yi haɓɓakar ba-zata a ƙarshen 2024

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai-tsaye.

Isra'ila na neman Syria ta janye dakarunta daga kudancin ƙasar

Talata 25 Faburairu, 2025 da 4:53:09 Yamma

Buƙatar ka iya jawo rikici tsakanin Isra'ila da sabuwar gwamnati a Syria bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad.

An ci ƙwallo takwas a wasan Barca da Atletico a Copa del Rey

Talata 25 Faburairu, 2025 da 11:07:07 Yamma

Barcelona da Atletico Madrid sun tashi 4-4 a wasan farko zagayen daf da karshe a Copa del Rey ranar Talata a Estadi Olimpic Lluis Companys.

Chelsea ta koma cikin ƴan huɗun farko a teburin Premier League

Talata 25 Faburairu, 2025 da 10:45:08 Yamma

Chelsea ta doke Southampton 4-0 a wasan mako na 27 a Premier League ranar Talata a Stamford Bridge.

Ban fitar da ran lashe Premier League na bana ba - Arteta

Talata 25 Faburairu, 2025 da 3:52:03 Yamma

Mikel Arteta ya ce Arsenal ce za ta lashe kofin Premier League na kakar nan, ba yadda ake hasashen Liverpool ba.

Ƙwazon Salah zai yi tsada lokacin tsawaita yarjejeniya a Liverpool

Talata 25 Faburairu, 2025 da 5:01:36 Yamma

Koci, Arne Slot ya ce ƙwazon da Mohamed Salah ke yi a wasannin bana, zai kara yin tsada idan Liverpool za ta tsawaita ƙwantiraginsa.

Lookman zai bar Atlanta, Man City na son Wirtz

Talata 25 Faburairu, 2025 da 3:59:57 Safiya

Manchester City na son dan wasan tsakiya na Jamus mai taka leda a Bayer Leverkusen, Florian Wirtz, 21, da kuma dan wasan tsakiya na Ingila James McAtee,

Me Nasir El-Rufa'i ke nema a siyasance?

Talata 25 Faburairu, 2025 da 3:54:21 Safiya

Tambayar kenan da an Najeriya ke yi cewa me Malam Nasir ElRufa'i ke nema a siyasance ne, tun bayan wata tattaunawa irinta ta farko da ya yi da yammacin Litinin inda ya ce shi ba zai taɓa komawa jam'iyyar PDP ba sannan kuma shi har yanzu ɗan jam'iyyar APC ne.

Ba ni da lokacin yin cacar baka da El-Rufa'i – Ribadu

Talata 25 Faburairu, 2025 da 8:27:03 Safiya

Mai bai wa shugaban na Najeriya shawara kan tsaro ya ƙara da cewa ya kame daga faɗin abubuwa marasa daɗi ga tsohon gwamnan ne bisa la'akari da irin dangantakarsu.

Ɗanƙwallon Najeriya Abubakar Lawal ya rasu bayan faɗowa daga bene

Talata 25 Faburairu, 2025 da 9:28:33 Safiya

Rundunar 'yansanda ta ƙasar Uganda ta ce tana bincike game da mutuwar wani ɗanƙwallon ɗan Najeriya mai suna Abubakar Lawal, wanda ya faɗo daga saman ginin wani kantin sayar da kayayyaki.

Daga ina Hezbollah ke samun kuɗaɗenta?

Talata 25 Faburairu, 2025 da 3:54:45 Safiya

Hanyar da ƙungiyar mayakan Hezbollah na Lebanon ke samun kuɗaɗenta na sake fuskantar sabbin nazari, bayan wani harin sama da Israi'la ta kai a ƙarshen shekarar da ta gabata kan wata ƙungiyar hada-hadar kuɗi da ke da alaƙa da ƙungiyar.

Muna sa ran kawo ƙarshen yaƙi a wannan shekarar - Zelensky

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye.

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da ƴan majalisar tarayya huɗu daga jihar Kano

Litinin 24 Faburairu, 2025 da 2:38:36 Yamma

A bayanin da ya yi wa manema labaru a ranar Litinin a Kano, shugaban jam'iyyar, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce jam'iyyar ta ɗauki matakin ne bayan samun ƴan majalisar da laifin ayyukan zagon ƙasa ga jam'iyyar.

Yadda 'Turji ya kafa sabuwar daba' a wani yanki na Sokoto

Litinin 24 Faburairu, 2025 da 6:36:02 Yamma

Al'ummar yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoton sun ce yanzu haka Bello Turji ya kafa sabuwar daba a yankinsu, inda ya ke tura yaransa su aikata ɓarna a ƙauyukan yankin.

Sojojin Sudan sun ƙwace birnin el-Obeid daga hannun RSF

Litinin 24 Faburairu, 2025 da 12:22:14 Yamma

Sojojin Sudan sun ce sun kawo ƙarshen iko da birnin el-Obeid na yankin kudancin ƙasar na kusan shekaru biyu da dakarun RSF suka yi.

Zan bar APC idan aka sake zaɓar Abdullahi Abbas shugaban jam'iyyar - Ata

Talata 25 Faburairu, 2025 da 3:55:23 Safiya

Ministan Ma'aikatar gidaje Yusuf Abdullahi Ata ya ce yana nan daram kan bakarsa na yakar duk wasu kalamai da za su iya kai ga rashin nasarar jam'iyyar.

Wane ne Aristotle shahararren masanin falsafa na duniya?

Lahadi 23 Faburairu, 2025 da 5:04:37 Yamma

Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka taɓa gani a doron ƙasa? Fitaccen malamin Falsafa ɗan Birtaniya, John Sellars na ganin haka.

Gwamnan Kano nake son zama ba shugaban jam'iyyar APC ba - Abbas

Litinin 24 Faburairu, 2025 da 3:54:51 Safiya

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya ce sun yi mamakin dalilan da suka sa Yusuf Abdullahi Ata ya fara maganar ba sa son shi a matsayin shugaban jam'iyyar APC, bayan shi burinsa ya zama gwamnan Kano.

Shin ko Turai za ta iya kare kanta ba tare da Amurka ba?

Litinin 24 Faburairu, 2025 da 3:55:43 Safiya

Yadda Amurka ta sauya manufarta ya tayar da hankalin shugabannin turai kuma wannan ne ya sa aka shirya taron gaggawa a ranar 17 ga watan Fabrairu a birnin Paris domin tattauna rikicin Ukraine da tsaron nahiyar.

Yadda Iran ta yi watsi da sansanonin sojinta da ke Syria

Litinin 24 Faburairu, 2025 da 3:55:14 Safiya

BBC ta yi nazari kan ruɗanin da aka fuskanta yayin da Iran ta yi watsi da sansanonin sojinta a Syria.

Isra'ila ta dakatar da sakin fursunonin Falasɗinawa har sai abin da hali ya yi

Lahadi 23 Faburairu, 2025 da 1:19:41 Yamma

Falasɗinawa sama da 600, a wani lamari da zai kawo tsaiko kan yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza.

Mun ci ƙarfin shirye-shiryen aikin Hajjin bana - NAHCON

Lahadi 23 Faburairu, 2025 da 3:58:16 Safiya

Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta ce ta kammala tantance adadin maniyyatan da za su sauke farali a bana da, da jiragen da za su yi jigilarsu da sauran muhimman abubuwan da suka jiɓanci aikin hajjin.

Waiwaye: Karyewar farashin abinci da tankiyar Sanata Akpabio da Natasha

Lahadi 23 Faburairu, 2025 da 3:57:54 Safiya

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Lafiyar ƙwaƙwalwa: Abubuwan da za ku yi don samun farin ciki

Lahadi 23 Faburairu, 2025 da 3:56:56 Safiya

Sauye-sauye ƴan ƙalilan ka iya inganta rayuwarku

APC ta ayyana ranar gudanar da taron masu ruwa da tsaki

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, Lahadi, 22/02/2025

Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

__

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, Lahadi, 23/02/2025

Amsoshin Takardunku 23/02/2025

Lahadi 23 Faburairu, 2025 da 3:52:06 Yamma

Amsoshin Takardunku, shiri ne na BBC Hausa da ke amsa tarin tambayoyin da kuke aiko mana, domin ilimantarwa da wayar da kai.

Hikayata: Labarin Mafitarmu 23/02/2025

Lahadi 23 Faburairu, 2025 da 1:37:47 Yamma

Wannan labari na Mafitarmu an yi shi ne a kan faɗakar da jama'a kan sanin illolin sare da ji da kuma amfanin dajin ga rayuwar ɗan'Adam da sauran halittu da ma duniyar baki ɗaya.

Lafiya Zinariya: Illolin na'urorin fasahar zamani ga yara

Asabar 22 Faburairu, 2025 da 1:39:53 Yamma

Lafiya Zinariya: Illolin na'urorin fasahar zamani ga lafiyar ƙwaƙwalwa da ta gangar jikin yara.

Gane Mini Hanya : Shirin Hajjin bana 22/02/2025

Asabar 22 Faburairu, 2025 da 2:16:51 Yamma

Shugaban hukumar aikin Hajjin Najeriya ya yi bayani kan taƙaddamar da ke tsakanin hukumar da wani kamfanin Saudiyya da kuma shirye-shirye kan Hajjin 2025.

Ra'ayi Riga: Yadda dakatar da tallafin USAID zai shafi Najeriya 21/02/2025

Asabar 22 Faburairu, 2025 da 2:09:29 Yamma

A ranar 13 ga watan Fabrairu ne wani ɗan majalisar Amurka, Scott Perry ya zargi USAID da tallafa wa ƙungiyoyin ta'addanci a ƙasashen duniya, ciki har da Boko Haram.

Mitocin da muke watsa shirye-shiryenmu

Jummaʼa 8 Disamba, 2023 da 6:50:55 Yamma

Sashen Hausa na BBC na watsa shirye-shirye guda huɗu a kowace rana, na tsawon minti talatin-talatin cikin harshen Hausa.